102

1 Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
2 Har kuka ziyarci kaburbura.
3 A´aha! (Nan gaba) zã ku sani.
4 Sa´an nan, tabbas, zã ku sani.
5 Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
6 Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
7 Sa´an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
8 Sa´an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni´imar (da aka yi muku).