15

1 A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
2 Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.(1)
3 Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa´an nan da sannu zã su sani.
4 Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
5 Wata al´umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
6 Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur´ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
7 "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã´ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"
8 Bã Mu sassaukar da malã´iku fãce da gaskiya,(2) bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
9 Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur´ãni), kuma lalle Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayħwane gare shi.
10 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.
11 Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
12 Kamar wancan ne Muke shigar da shi(3) a cikin zukãtan mãsu laifi.
13 Bã su yin ĩmãni da shi,(4) kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
14 Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
15 Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. ôa, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."
16 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
17 Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
18 Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
19 Kuma ƙasa Mun mĩkħ ta kuma Mun jħfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikħli.
20 Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã(1) da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
21 Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
22 Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa´an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacħwa a gare shi ba.
23 Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashħwa kuma Mũ ne magada.
24 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
25 Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
26 Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
27 Kuma Aljani Mun haliccħ shi daga gabãni, daga wutar (2) iskar zafi.
28 Kuma a l?kacin da Ubangijinka ya ce wa mal?´iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙeƙasasshen yumɓu wanda ya canja."
29 "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa(3) a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
30 Sai malã´iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
31 Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancħwa daga mãsu yin sujadar.
32 Ya ce: "Yã Iblĩs mħne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"
33 Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."
34 Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."
35 "Kuma lalle ne akwai la´ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."
36 Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."
37 Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
38 "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."
39 Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."
40 "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."
41 Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."
42 "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."
43 Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma´alkawartarsu gabã ɗaya.
44 Tanã da ƙõfõfi bakwai,(1) ga kõwace ƙõfa akwai wani juz´i daga gare su rababbe.
45 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
46 "Ku shigħ ta da aminci, kunã amintattu."
47 Kuma Muka ɗħbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama ´yan´uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
48 Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga cikinta ba.
49 Ka bai wa bãyiNa lãbari cħwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
50 Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.
51 Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.
52 A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."
53 Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi maka bushãra game da wani yãro masani."
54 Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra(1) ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
55 Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
56 Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?"
57 Ya ce: "To, mħne ne babban al´amarinku? Yã kũ manzanni!"
58 Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."
59 "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
60 "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cħwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
61 To, a lõkacin da mazannin suka jħ wa mutãnen Lũɗu,
62 Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."
63 Suka ce: "ôa, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."
64 "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
65 "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka umurce ku."
66 Kuma Muka hukunta wancan al´amarin zuwa gare shi cħwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankħwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
67 Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
68 Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."
69 "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
70 Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"
71 Ya ce: "Ga waɗannan ´ya´yãna (1) idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
72 Rantsuwa da(2) rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
73 Sa´an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
74 Sa´an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
75 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
76 Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a għfen wata hanyã tabbatacciya.(3)
77 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
78 Kuma lalle ne ma´abũta Al´aika(4) sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
79 Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a għfen wani tafarki mabayyani.
80 Kuma lalle ne haƙĩƙa ma´abũta Hijiri(5) sun ƙaryata Manzanni.
81 Kuma Muka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirħwa daga gare su.
82 Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
83 Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
84 Sa´an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
85 Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã´a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
86 Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
87 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu(6) da Alƙur´ãni mai girma.
88 Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau´i-nau´i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
89 Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."
90 Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,(7)
91 Waɗanda suka sanya Alƙur´ãni tãtsuniyõyi.
92 To, rantsuwa da Ubangijinka! (1) Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
93 Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
94 Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
95 Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu(2) izgili.
96 Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa´an nan da sannu zã su sani.
97 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cħwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
98 Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
99 Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.