16

1 Al´amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nħmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
2 Yanã sassaukar da malã´iku da Rũhi(3) daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cħwa ku yi gargaɗi cħwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
3 Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
4 Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
5 Da dabbõbin ni´ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
6 Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.
7 Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai.
8 Kuma da dawãki(1) da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.
9 Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacħwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya.
10 Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo.
11 Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan ´yã´yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
12 Kuma Ya hõrħ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta.
13 Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa.
14 Kuma Shĩ ne Ya hõrħ tħku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nħman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdħwa.
15 Kuma Ya jħfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa.
16 Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nħman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci).
17 Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa?
18 Kuma idan kun ƙidãya ni´imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
19 Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa.
20 Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa.
21 Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba.
22 Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne.
23 Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai.
24 Idan aka ce musu: "Mħne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko."
25 Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar Ƙiyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.
26 Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa,(1) sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jħ musu daga inda ba su sani ba.
27 Sa´an nan a Rãnar Ƙiyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cħwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha´aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai."
28 Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jħfa nħman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
29 Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa´an nan tir da mazaunin mãsu girman kai.
30 Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mħne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "alhħri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhħri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa.
31 Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa.
32 Waɗanda malã´iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã´ikun sunã cħwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
33 Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã´iku su jħ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
34 Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.
35 Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?
36 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al´umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci Ɗãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa´an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
37 Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka.
38 Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cħwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na´am, Yanã tãyarwa. Wa´adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
39 Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cħwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã.
40 Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yanã kasancħwa.
41 Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha´anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhħri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani.
42 Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
43 Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
44 Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni.
45 Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba?
46 Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba.
47 Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
48 Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai?
49 Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala´iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara.
50 Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su.
51 Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa´an nan sai kuji tsõroNa, Ni kawai."
52 Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa?
53 Kuma abin da yake a gare ku na ni´ima, to, daga Allah ne. Sa´an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa.
54 sa´an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sunã shirki.
55 Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa´an nan da sannu zã ku sani.
56 Kuma sunã sanya rabõ(1) ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa.
57 Kuma sunã danganta ´ya´ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha´awa.
58 Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace(2) sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki.
59 Yanã ɓõyħwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana.
60 Ga waɗanda ba su yi ĩmãni (3) da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
61 Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu,(4) dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa´an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa´a guda, kuma bã zã su gabãta ba.
62 Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cħwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlħwa ne (a cikinta) .
63 Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al´ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
64 Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
65 Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre.
66 Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni´ima;Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã.
67 Kuma daga ´ya´yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye(1) da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.
68 Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi(2) zuwa ga ƙudan zuma cħwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."
69 "Sa´an nan ki ci daga dukan ´ya´yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
70 Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa´an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.
71 Kuma Allah Ya fifita sãshenku(3) a kan sãshe a arziki. Sa´an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni´imar Allah suke musu?
72 Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni´imar Allah sũ, suke kãfirta?
73 Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme) .
74 Sa´an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba.
75 Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa´an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. ôa mafi yawansu ba su sani ba.
76 Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bħbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhħri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?
77 Kuma ga Allah gaibin(1) sammai da ƙasa yake, kuma al´amarin Sã´a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne.
78 Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde.
79 Shin ba su ga tsuntsãye(2) ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
80 Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni´ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu(1) da gãshinsu da għzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
81 Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna(2) sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni´imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.
82 To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã.
83 Suna sanin ni´imar Allah, sa´an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne.
84 Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al´umma, sa´an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nħman kõmawarsu ba.
85 Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa´an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba.
86 Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwan shirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jħfa magana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne."
87 Kuma su shiga nħman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su.
88 Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Alla, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi.
89 Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al´umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãfi a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi).
90 Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma´abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama´a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa.
91 Kuma ku cika da alkãwarin(1) Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncħwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.
92 Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancħwar wata al´umma tãfi rĩba daga wata al´umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar Ƙiyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũna.
93 Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al´umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. Kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
94 Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma.(1)
95 Kada ku sayi ´yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhħri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.
96 Abin da yake a wurinku yanã ƙãrħwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
97 Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
98 Sa´an nan idan ka karantã(2) Alƙur´ãni, sai ka nħmi tsari ga Allah daga shaiɗan jħfaffe.
99 Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu.
100 Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne.
101 Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, maƙirƙiri ne." ôa, mafi yawansu bã sa sani.
102 Ka ce: "Rũhul Ƙudusi(3) ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma(dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi."
103 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cħwa) lalle ne sũ, sunã cħwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatar da maganar zuwa gare shi, Ba´ajame (1) ne, kuma wannan (Alƙur´ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne.
104 Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allah bã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
105 Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata.
106 Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa,(2) fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma.
107 Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
108 Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu.
109 Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra.
110 Sa´an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa´an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta(3) haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
111 A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗħwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba.
112 Kuma Allah Ya buga misãli,(1) wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni´imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã´antãwa.
113 Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jħmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
114 Sa´an nan ku ci daga(2) abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni´imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.
115 Abin sani kawai (Allah) Ya haramta(3) muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa´an nan wanda aka tĩlasta a kan jama´a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
116 Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba.
117 Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
118 Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni,(4) kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
119 Sa´an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki(1) da jãhilci, sa´an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
120 Lalle ne Ibrãhĩm(2) ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
121 Mai gõdiya(3) ga ni´imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.
122 Kuma Muka ba shi alhħri a cikin dũniya. Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai.
123 Sa´an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cħwa), "Ka(4) bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.´
124 Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wa jũna a cikin sha´aninsa.(5) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa,Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar Ƙiyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.
125 Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima(6) da wa´azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
126 Kuma idan kuka sãka(7) wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhħri ga mãsu haƙuri.
127 Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci.
128 Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne.