21

1 Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirħwa.
2 Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa.
3 Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cħwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jħ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?"
4 Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani."
5 ôa, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. ôa, yã ƙirƙira shi ne. ôa, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko."
6 Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?
7 Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma´abũta ambato(1) idan kun kasance ba ku sani ba.
8 Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.
9 Sa´an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsħrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa.(2)
10 Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku,(3) a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta?
11 Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta.
12 Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta.
13 "Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni´imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku."
14 Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."
15 Sa´an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da´awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu.
16 Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba.
17 Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun(1) riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.
18 ôa, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa.
19 Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã´iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya.
20 Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni.
21 Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)?
22 Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al´arshi daga abin da suke siffantãwa.
23 Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su.
24 Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. ôa, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirħwa ne."
25 Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cħwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini."
26 Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! ôa, (malã´iku) bãyi ne mãsu daraja.
27 Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki.
28 Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cħto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa.
29 Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai.
30 Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cħwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,(1) sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba?
31 Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa.
32 Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirħwa ne.
33 Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu(2) a cikin wani sarari suKe iyo.
34 Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama?
35 Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhħri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.
36 Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cħwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta(1) ne.
37 An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nħmiyin gaggãwa.
38 Kuma sunã cħwa, "A yaushe wannan wa´adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?"
39 Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba.
40 ôa, tanã jħ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa´an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba.
41 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su.
42 Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" ôa, sũ mãsu bijirħwa ne daga ambaton Ubangijinsu.
43 Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su(2) ba daga gareMu.
44 ôa, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni´imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cħwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage(3) ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya?
45 Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi.
46 Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cħwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."
47 Kuma Munã aza ma´aunan ãdalci ga Rãnar Ƙiyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi.
48 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa.
49 Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa´a.
50 Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi?
51 Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi.
52 Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mħne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?"
53 Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu."
54 Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna."
55 Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?"
56 Ya ce: "ôa, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka."
57 "Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya."
58 Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.
59 Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai."
60 Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm."
61 Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida."
62 Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!"
63 Ya ce: "ôa, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana."
64 Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai."
65 Sa´an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana."
66 Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?"
67 "Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?"
68 Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa."
69 Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm."
70 Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra.
71 Kuma Muka tsħrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai.
72 Kuma Muka ba shi Is´haka da Ya´aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai.
73 Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhħri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu.
74 Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai.
75 Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai.
76 Kuma Nũhu, a sa´ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa´an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma.
77 Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
78 Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa´ad da suke yin hukunci a cikin sha´anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu.
79 Sai Muka fahimtar da ita (mats´alar)(1) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.
80 Kuma Muka sanar da shi sana´ar(2) wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdħwa ne?
81 Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme.
82 Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su.
83 Kuma da Ayyũba a sã´ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama."
84 Sai Muka karɓa masa, sa´an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa(1) ga mãsu ibãda.
85 Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri.
86 Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai.
87 Kuma mai kifi(2) a sã´ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cħwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cħwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."
88 Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni.
89 Kuma da Zakariyya a sa´ad da ya kirãyi Ubangijinsa cħwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhħrin mãsu gãdo."
90 Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata(3) masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsħre zuwa ga ayyukan alhħri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu.
91 Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.(1) Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.
92 Lalle ne wannan(2) ita ce al´ummarku ta zama al´umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.
93 Kuma suka kakkãtse al´amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni
94 Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.
95 Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cħwa lalle sũ, bã su kõmõwa.
96 Har sa´ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.
97 Kuma wa´adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cħwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! ôa, mun kasance dai mãsu zãlunci!"
98 (A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin(3) da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."
99 Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.
100 Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.
101 Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garħ su daga garħ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.
102 Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa.
103 Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã´iku na yi musu marãba (sunã cħwa) "Wannan yininku nħ wanda kuka kasance anã yi muku wa´adi da shi."
104 A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗħwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon(1) halitta Muke mãyar da ita. Wa´adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.
105 Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato(2) (Lauhul Mahfũz) cħwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta.
106 Lalle ne a cikin wannan (Alƙur´ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta(3) ga waɗansu mutãne mãsu ibãda.
107 Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.
108 Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cħwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?"
109 Sa´an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa´adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?"
110 "Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyħwa.
111 "Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci."
112 Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nħman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa."