37

1 Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
2 Sa´an nan mãsu yin tsãwa(1) dõmin gargaɗi.
3 Sa´an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
4 Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa Ɗaya ne.
5 Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
6 Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
7 Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
8 Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama´a mafi ɗaukaka (Malã´iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane għfe.
9 Dõmin tunkuɗħwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
10 Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
11 Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
12 ôa, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
13 Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
14 Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
15 Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
16 "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa,ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
17 "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
18 Ka ce: "Na´am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
19 Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
20 Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
21 Wannan ita ce rãnar rarrabħwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
22 Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
23 Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
24 Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
25 Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
26 ôa, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
27 Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
28 Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jħ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
29 Suka ce: "ôa, ba ku kasance mũminai ba.
30 "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. ôa, kun kasance mutãne ne mãsu kħtare iyãka."
31 "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
32 "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
33 To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
34 Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
35 Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
36 Kuma sunã cħwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
37 ôa, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
38 Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
39 Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
40 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
41 Waɗannan sunã da abinci sananne.
42 ´Ya´yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
43 A cikin gidãjen Aljannar ni´ima.
44 A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
45 Anã kħwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marħmari.
46 Farã mai dãɗi ga mashãyan.
47 A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
48 Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
49 Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
50 Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
51 Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
52 Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
53 "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
54 (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
55 Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
56 Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
57 "Kuma bã dõmin ni´imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
58 "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
59 "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"
60 Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
61 Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
62 Shin wancan shĩ ne mafi zama alhħri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
63 Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
64 Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
65 Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
66 To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa´an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
67 Sa´an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
68 Sa´an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
69 Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
70 Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
71 Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
72 Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
73 Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
74 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
75 Kuma lalle, haƙĩƙa´ Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
76 Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
77 Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
78 Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama´ar ƙarshe.
79 Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
80 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
81 Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
82 Sã´an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
83 Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
84 A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
85 A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mħne ne kuke bautãwa?"
86 "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
87 "To, mħne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
88 Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
89 Sã´an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
90 Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
91 Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa´an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
92 "Me ya sãme ku, bã ku magana?"
93 Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
94 Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
95 Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
96 "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
97 Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa´an nan ku jħfa shi a cikin Jahĩm."
98 Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
99 Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
100 "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
101 Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro(1) mai haƙuri.
102 To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mħ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."
103 To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga għfen gõshinsa.
104 Kuma Muka kira shi cħwa "Ya Ibrahĩm!"
105 "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
106 Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
107 Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
108 Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
109 Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
110 Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
111 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
112 Kuma Muka yi masa bushãra(1) Da Is´hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
113 Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is´hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
114 Kuma lalle, Mun yi ni´ima ga Mũsã da Hãrũna.
115 Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
116 Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
117 Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
118 Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
119 Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
120 Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
121 Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
122 Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
123 Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
124 A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
125 "Shin, kunã bauta wa Ba´al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
126 "Allah Ubangijinku,kuma Ubangijin ubanninku farko?"
127 Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
128 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
129 Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
130 Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
131 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
132 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
133 Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
134 A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
135 Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
136 Sã´an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
137 Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
138 Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
139 Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
140 A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
141 Sã´an nan ya yi ƙuri´a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
142 Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
143 To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
144 Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
145 Sai Muka jħfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
146 Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
147 Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
148 Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
149 Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da ´ya´ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
150 Kõ kuma Mun halitta malã´iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
151 To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cħwa.
152 "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
153 Shin, Yã zãɓi ´yã´ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
154 Mħ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
155 Shin, bã ku tunãni?
156 Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
157 To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
158 Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
159 Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
160 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
161 To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
162 Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
163 Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
164 "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,(1) fãce yanã da matsayi sananne."
165 "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
166 "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
167 Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cħwa,
168 "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
169 "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
170 Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
171 Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
172 Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
173 Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
174 Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
175 Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.(2)
176 Shin fa, da azabarMu suke nħman gaggãwa?
177 To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
178 Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
179 Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
180 Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
181 Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
182 Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.