55

1 (Allah) Mai rahama.
2 Yã sanar da Alƙur´ani.
3 Yã halitta mutum.
4 Yã sanar da shi bayãni (magana).
5 Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
6 Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu´i.
7 Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikħli.
8 Dõmin kada ku karkatar da sikħlin.
9 Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikħlin.
10 Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
11 A cikinta akwai ´ya´yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
12 Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
13 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangjinku(1) kuke ƙaryatãwa?
14 Yã halitta mutum daga ƙħkasasshen yumɓu kumar kasko.
15 Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
16 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
17 Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
18 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
19 Yã garwaya tħku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
20 A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
21 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
22 Lu´ulu´u da murjãni na fita daga gare su.
23 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
24 Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tħku kamar manyan duwãtsu.
25 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
26 Dukkan wanda ke kanta(1) mai ƙãrħwa ne.
27 Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
28 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
29 wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha´ani.
30 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
31 Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ(2) mãsu nauyin halitta biyu!
32 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
33 Ya jama´ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcħwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcħwaba fãce da wani dalĩli.
34 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
35 Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nħmi taimako ba?
36 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
37 Sa´an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
38 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
39 To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
40 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
41 zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
42 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
43 Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
44 Sunã kħwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
45 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
46 Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
47 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
48 Mãsu rassan itãce.
49 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
50 A cikinsu akwai marħmari biyu sunã gudãna.
51 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
52 A cikinsu akwai nau´i biyu daga kõwane ´ya´yan itãcen marmari.
53 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
54 Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun ´yã´yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
55 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
56 A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
57 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
58 Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
59 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
60 Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (ôaha) fãce kyautatãwa.
61 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
62 Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
63 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
64 Mãsu duhun inuwa.
65 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
66 A cikinsu akwai marħmari biyu masu kwarãrar ruwa.
67 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
68 A cikinsu akwai ´ya´yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
69 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
70 A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
71 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
72 Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
73 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
74 Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗħbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
75 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
76 Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
77 To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
78 Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.