7

1 A. L̃. M̃. Ṣ̃.
2 Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.
3 Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.
4 Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jħ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla.
5 Sa´an nan bãbu abin da yake da´awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jħ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci,"
6 Sa´an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin.
7 Sa´an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakuwa ba.
8 Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikħlansa suka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.
9 Kuma wanda sikħlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci.
10 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdħwa.
11 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa´an nan kuma Mun sũrantã ku, sa´an nan kuma Mun ce wa malã´iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.(1)
12 Ya ce: "Mħne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, a l?kacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka."
13 Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; d?min b? ya kasancħwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci."
14 Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar(1) da su."
15 Ya ce: "Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri."(2)
16 Ya ce: "To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici."
17 "Sa´an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba."
18 Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya."
19 "Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci Wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai."
20 Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al´aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã´iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama."
21 Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne.
22 Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa´an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al´aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?" ,
23 Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancħwa daga mãsu hasãra."
24 Ya ce: "Ku sauka, s?shenku zuwa ga s?she yan? maƙiyi, kuma kun? da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin d?ɗi zuwa ga wani l?kaci."
25 Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku."
26 Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa(1) a kanku, tanã rufe muku al´aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhħri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!
27 Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al´aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanya Shaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.
28 Kuma idan suka aikata alfãsha(2) su ce: "Mun sãmi ubanninmu a kanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?"
29 Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙħ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa."
30 Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne.
31 Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna.
32 Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani.
33 Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwan alf?sha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama´a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."
34 Kuma ga kõwace al´umma akwai ajali. Sa´an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa´a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba.
35 Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jħ muku, sunã gaya muku ay?yiNa - to, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki.
36 Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne.
37 To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cħwa lalle sũ, sun kasance kãfirai."
38 Ya ce: "Ku shiga a cikin al´ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al´umma ta shiga sai ta la´ani ´yar´uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane(1) akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."
39 Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tsirfawa!"
40 Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi.
41 Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai.
42 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.
43 Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jħ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cħwa: "Waccan Aljanna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
44 Kuma ´yan Aljanna suka kirãyi ´yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa´adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa´adi, gaskiya?" Suka ce: "Na´am." Sai mai sanarwa ya yi yħkuwa, cħwa: "La´anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."
45 "Waɗanda suke kangħwa daga hanyar Allah, kuma sunã nħman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne."
46 Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki,(1) kuma a kan A´arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljanna cħwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.
47 Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai."
48 Kuma abõkan A´araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?"
49 "Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro a kanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba."
50 Kuma ´yan wuta suka kirãyi ´yan Aljanna cħwa: "Ku zubo a kanmu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai."
51 "Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu.
52 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jħ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani.
53 Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda suka manta da Shi daga gabãni, sunã cħwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu sun jħ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cħto, su yi cħto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu.
54 Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa´an nan kuma Ya daidaita a kan Al´arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nħman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!
55 Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsu wuce iyãka.
56 Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa.
57 Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi,(1) sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa´an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa´an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan ´ya´yan itace. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni.
58 Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗanda suke gõdħwa.
59 Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnħnsa, sai ya ce: "Yã mutãnħna! Ku bauta wa Allah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yi muku tsõron azãbar wani Yini mai girma."
60 Mashawarta(1) daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya."
61 Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu !"
62 "Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba.
63 "Shin, kunã mãmãkin cħwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku?"
64 Sai suka ƙaryata shi, sa´an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu.
65 Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan´uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"
66 Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata."
67 Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!"
68 Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce.
69 "Shin, kuma kun yi mãmãki cħwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayħwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni´imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara."
70 Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa´adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
71 Ya ce: "Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne."
72 To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminai ba.
73 Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan´uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku."
74 "Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni´imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi."(1)
75 Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar,(2) ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: "Shin, kunã sanin cħwa Sãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin da aka aiko shi, mãsu ĩmãni ne."
76 Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne."
77 Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa´adi da shi, idan kã kasance daga manzanni !"
78 Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne!
79 Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku da manzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha!"
80 Da Lũɗu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa: "Shin, kunã jħ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?"
81 "Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jħ wa maza da sha´awa, baicin mata; ôa, kũ mutãne ne maɓarnata."
82 Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasu mutãne ne mãsu da´awar tsarki!"
83 Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa.
84 Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance!
85 Kuma zuwa Madayana ɗan´uwansu Shu´aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kuma kada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhħri a gare ku, idan kun kasance mũminai."
86 "Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacħwa, kuma kunã kangħwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nħman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance:"
87 "Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhħrin mãsu hukunci."
88 Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu´aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?"
89 "Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhħrin mãsu hukunci."
90 Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu´aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne."
91 Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne.
92 Waɗanda suka ƙaryata Shu´aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu´aibu, sun kasance sũ ne mãsu hasãra!
93 Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?"
94 Kuma ba Mu aika wani Annabi(1) a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai.
95 Sa´an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." ( Sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancħwa."
96 Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa.
97 Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jħ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci?
98 Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jħ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa?
99 Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra!
100 Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cħwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji?
101 Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jħ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãni da abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufħwa a kan zukãtan kãfirai.
102 Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai.
103 Sa´an nan kuma Mun aika Musa,(1) daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir´auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take.
104 Kuma Musa ya ce: "Ya Fir´auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu."
105 "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã´ila tãre da ni."
106 Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
107 Sai ya jħfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!
108 Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!
109 Mashãwarta daga mutãnen Fir´auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi."
110 " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mħne ne kuke shawartawa?"
111 Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan´uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa.
112 "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi."
113 Kuma matsafa suka jħ wa fir´aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?"
114 Ya ce: "Na´am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta."
115 Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jħfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jħfãwa?"
116 Ya ce: "Ku jħfa." To a 1õkacin da suka jħfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jħ da tsafi mai girma."
117 Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cħwa: "Ka jħfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!
118 Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.
119 Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.
120 Kuma aka jħfar da matsafan, sunã mãsu sujada.
121 Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu."
122 "Ubangijin Mũsã da Harũna."
123 Fir´auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani."
124 "Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa´an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya."
125 Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne."
126 "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai!(1) "
127 Kuma mashawarta daga mutãnen Fir´auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne."
128 Mũsã ya ce wa mutãnensa:(2) "Ku nħmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce."
129 Suka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa´an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa."
130 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir´auna da tsananin shħkaru (fari) da nakasa daga ´ya´yan itãce; tsammãninsu sunã tunãwa.
131 Sa´an nan idan wani alhħri ya jħ musu, sai su ce: "Wannan nãmu ne," kuma idan masĩfa ta sãme su, sai su yi shu´umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi. To, shu´umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!"
132 Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba."
133 Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabħwa;(1) Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.
134 Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã´ila tare da kai."
135 To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarħwa!
136 Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tħku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai.
137 Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã´ĩla, sabõda abin da suka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir´auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã´antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa.(2)
138 Kuma Muka ƙħtarar da Banĩ Isra´ila ga tħku, sai suka jħ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa "(1) Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta."
139 "Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne."
140 Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nħma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?"
141 Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir´auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku,(2) Mai girma.
142 Kuma Muka yi wa´adi ga Mũsã da dare talãtin(3) kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba´in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan´uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi."
143 Kuma a lõkacin da Mũsã ya jħ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa´an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai."
144 Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya."
145 Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa´azi da rarrabħwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu;(1) zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai."
146 Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai.
147 Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?
148 Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi,(2) jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cħwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.
149 Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cħwa lalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancħwa daga mãsu hasãra."
150 Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nħmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan´uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan´uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai."
151 Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan´uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!"
152 Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya.
153 Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa´an nan suka tũba daga bãyansu kuma suka yi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
154 Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne.
155 Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba´in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhħrin mãsu gãfara."
156 "Kuma Ka rubũta mana alhħri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa´an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne."
157 "Waɗanda suke sunã bin Manzo,(1) Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla. yanã umurnin su da alhħri kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yanã halatta musu abũbuwa mãsu daɗi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, waɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka taimake shi, kuma suka bi haske wanda aka saukar tãre da shi, waɗannan ne mãsu cin nasara."
158 Ka ce: "Yã kũ mutãne!(2) Lalle ne nĩ manzon Allah ne zuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."
159 Kuma daga mutãnen(3) Mũsã akwai al´umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.
160 Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al´ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensa suka nħme shi, ga shãyarwa, cħwa: "Ka dõki dũtsen(1) da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." Kuma ba su zãluncħ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.
161 Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya,(2) kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: ´Saryarwa,´ kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa."
162 Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana(3) watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.
163 Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tħku, a lõkacin da suke ƙħtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar(4) ɗinsu jħre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.
164 Kuma a lõkacin da wata al´umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa´azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nħman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa."
165 To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci.
166 Sa´an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu."
167 Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar Ƙiyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
168 Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al´ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhħri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa.
169 Sai wasu´ yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar(1) wannan ƙasƙantacciya, sunã cħwa: "Zã a gãfarta mana. "Idan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cħwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alh ħri ga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?
170 Kuma waɗanda suke riƙħwa da littãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa.
171 Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse(1) sama da su, kamar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa."
172 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na´am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne."(2)
173 Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?"
174 Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa.
175 Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa(3) ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.
176 Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nħmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jħranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni.
177 Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta.
178 Wanda(4) Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
179 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. ôa, sũ ne mafi ɓacħwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.
180 Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau.(1) Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.
181 Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al´umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci.
182 Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
183 Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.
184 Shin, ba su yi Tunani ba, cħwa bãbu wata hauka ga ma´abucinsu? (2) shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.
185 Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?
186 Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa.
187 Sunã tambayar ka(3) daga Sa´a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ. Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." Sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."
188 Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãce abin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhħri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba face mai gargaɗi, kuma mai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni."
189 Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma´auranta, dõmin ya natsu zuwa gare(1) ta. Sa´an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa´an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance daga mãsu gõdiya."
190 To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki.
191 Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa?
192 Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka!
193 Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne!
194 Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa´an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!
195 Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafiya da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan(2) shirkinku sa´an nan kuma ku yi mini kaidi, sa´an nan kada ku saurãra mini."
196 "Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai,"
197 "Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka."
198 Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani.
199 Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhħri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai.(1)
200 Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nħmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.
201 Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra.
202 Kuma ´yan´uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa´an nan kuma bã su taƙaitãwa.
203 Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni."
204 Kuma idan an karanta(2) Alƙur´ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.
205 Kuma ka ambaci(3) Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõma bãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.
206 Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.