81

1 Idan rãna aka shafe haskenta
2 Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
3 Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
4 Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna(1) aka sakħ su wãwai, bã ga kõwa ba.
5 Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
6 Kuma idan tħkuna aka mayar da su wuta.
7 Kuma idan rãyuka aka haɗa(2) su da jikunkunansu.
8 Kuma idan wadda aka turbuɗe(3) ta da rai aka tambaye ta.
9 "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
10 Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
11 Kuma idan sama aka fħɗe ta.
12 Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
13 Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
14 Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
15 To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã(4) ba.
16 Mãsu gudu suna ɓũya.
17 Da dare idan ya bãyar da bãya.
18 Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
19 Lalle ne shi (Alƙur´ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
20 Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al´arshi.
21 Wanda ake yi wa ɗã´a (wato shugaban malã´iku) ne a can, amintacce.
22 Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
23 Kuma lalle ne, yã gan shi(5) a cikin sararin sama mabayyani.
24 Kuma shi, ga gaibi(6) bã mai rowa ba ne.
25 Kuma shi (Alƙur´ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la´ana, ba ce.
26 Shin, a inã zã ku tafi?
27 Lalle ne shi (Alƙur´ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
28 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
29 Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.