86

1 Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
2 To, mħ yã sanar da kai abin da ake cħwa mai aukõwa da dare?
3 Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.(1)
4 Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
5 To, mutum ya dũba, daga mħ aka halittã shi?
6 An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
7 Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
8 Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
9 Rãnar da ake jarrabawar asirai.
10 Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
11 Ina rantsuwa da sama ma´abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankħwa.
12 Da ƙasa ma´abũciyar tsãgħwa,(2)
13 Lalle ne shĩ (Alƙur´ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki(3)
14 Kuma shĩ bã bananci(4) bane
15 Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
16 Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
17 Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.