93

1 Inã rantsuwa da hantsi.
2 Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
3 Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
4 Kuma lalle ta ƙarshe(2) ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
5 Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
6 Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa´an nan Ya yi maka makõma?
7 Kuma Ya sãme ka bã ka da shari´ã, sai Ya shiryar da kai?
8 Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
9 Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
10 Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
11 Kuma amma ni´imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).