94

1 Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
2 Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
3 Wanda ya nauyayi bãyanka?
4 Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
5 To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
6 Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
7 Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
8 Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.