95

1 Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.(1)
2 Da Dũr Sĩnĩna(2) .
3 Da wannan gari(3) amintacce.
4 Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
5 Sa´an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
6 Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
7 To, bãyan haka mħ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin Ƙiyãma)?
8 Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?(4)