97

1 Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur´ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
2 To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Ƙadari?
3 Lailatul Ƙadari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
4 Mala´iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
5 Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.