80

1 Yã game huska(1) kuma ya jũya bãya.
2 Sabõda makãho yã je masa.
3 To, me ya sanar da kai cħwa watakila shi ne zai tsarkaka.
4 Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
5 Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
6 Sa´an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
7 To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
8 Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
9 Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
10 Kai kuma kã shagala ga barinsa!
11 A´aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
12 Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
13 (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
14 Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakħwa.
15 A cikin hannãyen mala´iku marubũta.
16 Mãsu daraja, mãsu ɗã´a ga Allah.
17 An la´ani mutum (kafiri). Mħ yã yi kãfircinsa!
18 Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
19 Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa´an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
20 Sa´an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
21 Sa´an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
22 Sa´an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
23 Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
24 To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
25 Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
26 Sa´an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
27 Sa´an nan, Muka tsirar da ƙwaya ,a cikinta.
28 Da inabi da ciyãwa.
29 Da zaitũni da itãcen dabĩno.
30 Da lambuna, mãsu yawan itãce.
31 Da ´yã´yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
32 Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
33 To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
34 Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan´uwansa.
35 Da uwarsa da ubansa.
36 Da mãtarsa da ɗiyansa.
37 Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha´ani da ya ishe shi.
38 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
39 Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
40 Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
41 Baƙi zai rufe su.
42 Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).