82

1 Idan sama ta tsãge.
2 Kuma idan taurãri suka wãtse.
3 Kuma idan tħkuna aka facce su.
4 Kuma idan kaburbura aka tõne su.
5 Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
6 Yã kai mutum! Mħ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
7 Wanda Ya halitta ka sa´an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
8 A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
9 A´aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
10 Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
11 Mãsu daraja, marubũta.
12 Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
13 Lalle ne, mãsu ɗã´ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni´ima.
14 Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
15 Zã su shigħ ta a rãnar sakamako.
16 Bã zã su faku daga gare ta ba.
17 Kuma mħ ya sanar da kai abin da ake cħ wa rħnar sakamako?
18 Sa´an nan, mħ ya sanar da kai abin da ake cħ wa rãnar sakamako?
19 Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al´amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.